Kamfanin Dillancin labarai na Ahlulbaiti{a.s}-abna-Ayatullahi Hashimi Rafsanjani a yayin ganawarsa da shugaban majalisr koli ta juyin musulunci a Iraki yace, basira da jaruntaka halaye ne na mutanen Iraki kuma sun tabbatar da hakan a lokacin juyayin Arba'in na bana; a cikin yanayin da kasar take na rashin tsaro amma hakan bai hana mutane kwarara ba zuwa karbala wanna alamace ta jaruntaka.
Hashimi Rafsanjani ya kara da cewa, tausai da girmamawa halayene wadanda Imaman Ahlulbaiti{a.s} suka koyar damu, don haka duk dan shi'a na gaskiya dole ya zamo mai tarbiyya da girmama sauran mazahabobi domin haka shine koyarwar Ahlulbait{a.s}.
A wani sashe na maganarsa yace, dole ne al'ummar musulmi su hada kai, musamman musulmin Iraki yace; ya kamata manyan maluman shi'a da sunna su lura da kyau a yanzu makiya addini sun hada yaki a tsakanin musulmi wanda hakan ya haifar da kungiyoyi irin su Da'ish, Boko Haram, Nusra, wahabiyanci da salafanci.
Yace; burin makiya shine karfafa gunkiyoyin yan ta'adda a kasashen musulmi domin su samu gindin zama da wawace dokiyoyin al'ummar musulmi.
A nasa bangaren Hujjatul islam Ammar Hakim yace; taron mutane sama da miliyan 20 a juyayin Arba'in na bana na nuni da soyayya da kauna ga Aba Abdullahi Hussain {a.s}
Da ya juya bangaren siyasar kasar Iraki yace; hadin kan shi'a da sunna shine makiya basu so kuma abun na bakanta masu rai, wanda hakan yasa suka haifar da kungiyoyin irin su Da'ish domin kawo tsoro a cikin zukatan al'umma
Daga karshe yace; hadin gwiwa tsakanin shi'a da kurdawa zai taimaka wurin tabbatar da zaman lafiya da kuma wanzar da Iraki kasa daya.ABNA